<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>328</hymn_number>
<title>Tafiyarmu A Duniya Ta Kusa Ƙarewa LW328</title>
<lyrics>[V1]
 1) Tafiyarmu a duniya ta kusa ƙarewa.
 I, kome nisan hanya, lalle ta kai gida.
 Ko duhu muka ratsa, gari zai waye can.
 Babu sauran dare kuma gun Immanuel.

[V2]
 2) Da jinƙai duk da ilmi, ya shirya hanyata,
 Har ko a cikin duhu na iske haskensa.
 Zan yi yabon Mai Sani, zan yi yabon Mai Yi.
 Farko ne shi da ƙarshen, shi Immanuel.

[V3]
 3) A zuciyar Almasihu, ƙauna ta yalwata,
 Ta fi ta duniva daɗi, kome ne daɗinta.
 Can Sama dai zan gane alamun ƙaunarsa.
 Bisa goshina sunansa, Yesu Immanuel.

[V4]
 4) Amarya, idanunta a wajen ango ne,
 Ai, ba ta duban wani, sai fuskarsa kaɗai.
 Ni haka, fuskar Yesu da jiki sokakke,
 Ɗan Rago ne zan duba, shi Immanuel.</lyrics>
</song>